Siga:v20260128

Gama-garin Ƙa’idojin Sirri na Xiaomi

An sabunta Gama-garin Ƙa’idojin Sirrinmu a ran 10 ga Oktoba, 2025.

Ɗan tsaya lura da yadda muke aiwatar da sirri, kuma ka sanar da mu idan kana da wata tambaya.

Taƙaitaccen bayani

1. Gabatarwa

2. Me ake nufi da bayanin mutum?

3. Wane bayanin mutum ne muke tattarawa kuma a kan waɗanne dalilai?

4. Ya ya muke yaɗa bayanan mutum ɗinka ga ɓangarori na uku?

5. Mene ne madogarar shari'a ta sarrafa bayanan mutum ɗinka?

6. Waɗanne matakan tsaro muke bi don kare bayanan mutum ɗinka?

7. Mene ne tsawon lokacin da ake adana bayanan mutum ɗinka?

8. Ta ya za ka iya gudanar da zaɓuɓɓukan sirrinka?

9. Mene ne haƙƙoƙin kariyar bayananka?

10. Ya za ka bi haƙƙin kariyar bayananka kuma ya za ka tuntuɓe mu?

11. Ya ya ake tura bayanan mutum ɗinka daga a da ƙasa zuwa ƙasa?

12. Ya ya ake kare ƙananan yara?

13. Shin dole ne sai ka yarda da wani sharaɗi da ƙa’idar ɓangarori na uku?

14. Ya ya muke sabunta Ƙa’dojin Sirri?

1. Gabatarwa

Sirri yana ɗaya daga cikin ginshiƙan ƙa’dojin Xiaomi, kuma kare sirrinka shi ne babbar manufarmu. Duk da cewa kaya ko sabis ɗin Xiaomi suna da ƙa’idojin sirru na kansu, mun samar da taƙaitaccen bayani na wasu muhimman abubuwa a wannan Gama-garin Ƙa’idodjin Sirri. Ta wannan hanya, kana iya samun dama ga bayanai cikin sauri a matakai biyu: a siga mai sauƙi da siga mai ƙarin bayani da fayyacewa ta hanyar waiwayar ƙa’idojin sirri na kaya da/ko sabis ɗin da kake muradi.

Ɗan lura cewa sarrafa bayanan mutum wanda Xiaomi ke aiwatarwa ka iya bambanta dangane da takamaiman kayayyaki da/ko sabis-sabis, da kuma fasalolin da ake amfani da su da tsarin saitin da kowane mai amfani ya zaɓa.

A ƙarshe dai, abu mafi kyau muke so ga dukkan masu amfani da mu. Idan kana da wasu tambayoyi game da yadda muke sarrafa bayanai kamar yadda aka taƙaita a cikin wannan Gama-garin Ƙa’idar Sirri, ɗan tuntuɓe mu ta https://privacy.mi.com/support don magance takamaiman tambayoyinka. Za mu yi farin cikin ji daga gare ka.

2. Me ake nufi da bayanin mutum?

A ƙarƙashin wannan Ƙa’idodjin Sirri, "bayanin mutum" na nufin bayanan da ake iya amfani da su kai tsaye ko a kaikaice don shaida wani mutum, ko dai daga wannan bayanin shi kaɗai, ko kuma idan aka haɗa wannan bayanin da wasu bayanai waɗanda ke samuwa ga Xiaomi game da wannan mutum, face idan wata takamaimar doka ta yankinka ta saɓa ma hakan. Ya ƙunshi bayanai kamar su suna, da bayanan tuntuɓa, da lambobin shaida, da bayanan wuri ko bayanan ganewa na kan intanet (misali, ID na Asusun Xiaomi). Za mu yi amfani da bayanin mutum ɗinka tare da bin wannan Ƙa’idojin Sirri sau da ƙafa.

3. Wane bayanin mutum ne muke tattarawa kuma a kan waɗanne dalilai?

3.1 Tattara bayanan mutum daga gare ka

Sarrafa bayanin mutum wanda Xiaomi ke aiwatarwa ka iya bambanta dangane da kayayyaki da/ko sabis-sabis, da kuma fasalolin da ake amfani da su da tsarin saitin da kowane mai amfani ya zaɓa. Don haka, a yayin amfani da kayayyaki ko sabis-sabis ɗinmu, za a sarrafa bayanan mutum ɗinka don samar maka da kayayyaki da/ko sabis-sabis ɗin ka zaɓa.

Duk da kana iya nemo ƙarin bayani a takamaiman ƙa’idojin sirri na kayayyaki da/ko sabis-sabi ɗin da kake amfani da su, babban dalilinmu na tattara bayanin mutum ɗinka shi ne don mu samar maka da kayayyaki da sabis-sabis ɗin da ka zaɓa. Don haka, yawancin bayanin da muke sarrafawa game da kai shi ne wanda ake buƙata don samar da waɗannan kayayyaki da sabis-sabis.

Dangane da sabis ɗin da ka zaɓa, muna iya tattara irn waɗannan bayanai masu zuwa:

3.1.1 Bayanin da ka ba mu

Za mu iya tattara duk bayanin mutum ɗin da ka ba mu, wanda ake buƙata ga sabis ɗin da ka zaɓa. Misali, kana iya samar da sunanka, da lambar wayar hannu, da adireshin imel, da adireshin isar da saƙo, da bayanin oda, da bayanan tura imboyis, da lambar asusun banki, da sunan mai asusun, da lambar katin kiredit, da sauran bayanai idan kana amfani da aiyukan siyarwar ɗai-ɗai na mi.com; kana iya daidaita kayan aiki ko bayanai idan kana amfani da sabis na Xiaomi Cloud; kana iya samar da jinsinka, da bayanan da suka shafi tsaro da sauran bayanai idan ka ƙirƙiri asusu; kana iya samar mana da laƙabinka, da adireshin imel, hotuna, bidiyo ko wasu bayanan da ake buƙata idan ka shiga harkar talla; kana kuma iya samar da suna, da lambar wayar hannu da kuma adireshi idan ka yi ma’amala da mu, ko abubuwanmu, ko tallarmu, ko idan ka ci wata kyauta.

3.1.2 Bayanin da muka tattara a lokacin da kake amfani da sabis

  • Bayani mai alaƙa da Na’ura ko SIM. Misali, IMEI/OAID, lambar GAID, lambar IMSI, adireshin MAC, lambar jerangiya, siga da nau'in tsarin na’ura, sigar ROM, sigar Android, ID na Android, ID na Sarari, kamfanin sadarwar katin SIM da wurin da ya ke, bayanin nuni na allo, bayanan madannin na'ura, bayanan maƙerin na'ura da sunan samfuri, lokacin kunna na’ura, kamfanin sadarwa, nau'in haɗi, bayanan manyan sassan na’ura, hanyar sayarwa da bayanan ta'ammali (kamar su ma'ajiyar CPU, amfani da batir, da kaifin hoto da yanayin zafi na na'ura, samfurin tabarau na kyamara, da adadin yawan tayar da allo ko buɗewa).

  • Takamaiman bayani wanda masu samar da sabis na ɓangare na uku da abokan hulɗar kasuwancinmu suka alaƙanta gare ka: Muna iya tattarawa da amfani da bayanai kamar su ID ɗin tallarka wanda masu samar da sabis na ɓangare na uku da abokan hulɗar kasuwanci suka alaƙanta gare ka.

  • Bayanin da ya danganci amfani da manhajarka, gami da bayanan ganewa na musamman na manhaja (misali VAID, OAID, AAID, ID na Nan take) da bayanan manhaja na asali kamar jerin manhaja, da bayanin ID ɗin manhaja, da sigar SDK, da saitunan sabunta tsarin na’ura, da saitunan manhaja (yanki, yare, agogo, allon haruffa), da lokacin da manhaja ta shiga/fita daga gaban fage, da tarihin matsayin manhaja (misali saukewa, dasawa, sabuntawa, sharewa).

  • Bayanin da aka ƙirƙira a yayin da kake amfani da sabis ɗin tsarin na’ura na Xiaomi, kamar bajoji, da kimantawa, da bayanan shigarka, da kuma tarihin burauzin a cikin Xiaomi Community; da saƙonninka na cikin Xiaomi Community (yana bayyana ne ga mai aikawa da mai karɓa kawai); da tarihin kunna odiyo da tambayoyin bincike a cikin sabis ɗin kiɗa; da abubuwan da aka so, da tsokaci, da abubuwan da aka fi so, da abubuwan da aka yaɗa, da tambayoyin bincike a cikin ayyukan jigogi; da yaren tsarin na’ura, da ƙasa da yanki, da matsayin hanyar sadarwa, da jerin manhaja a cikin Taskar Manhaja; da bayanan amfaninku, gami da yanki, da IP, da mai samar da ƙunshiya mai dacewa, da yawan canza bangon allo, da dube-duben allo, da yanayin dudduba hoto, da tsawon lokacin duba hoto, da dannawa da lokacin da aka ɗauka ga maƙalu, da biyan rajista a cikin Wallpaper Corousel.

  • Bayanin wuri (ga takamaiman sabis/fasaloli kaɗai): nau'ikan bayanai daban-daban a kan sahihin wuri ko ƙiyasin wurin da kake idan ka yi amfani da sabis-sabis masu alaƙa da wuri (kewaye, yanayi, Gano na’ura, etc.) Wannan bayanan na iya ƙunsar yanki, da lambar ƙasa, da lambar birni, da lambar hanyar sadarwar wayar hannu, da lambar ƙasar waya, da lambar sel, da bayanin lonjitut da latitud, da saitunan agogo, da saitunan harshe. Kana iya taƙaita damar ɗaiɗaikun manhajoji ga bayanin wuri a kowane lokaci a cikin Saituna > Manhaja > Izini > Izini > Wuri.

  • Bayanan rajistar ayyuka: bayanin da ya danganci yadda kake amfani da wasu fasaloli, da manhajoji, da shafukan yanar gizo. Wannan ka iya ƙunsar kukis da sauran fasahohin mai ganowa, da adiresoshin IP, da bayanin buƙatar hanyar sadarwa, da tarihin saƙo na wucin gadi, da bayanin gazawa ta kwatsam, da bayanin rajista wanda aka ƙirƙira ta hanyar amfani da wani sabis (kamar lokaci na rijista, da lokacin shiga, da lokacin aiki, dss.).

  • Sauran bayanai: darajar siffofin muhallin (ECV) (wato darajar da aka ƙirƙira daga ID na Asusun Xiaomi, da ID ɗin na'ura, ID na Wi-Fi ɗin da aka haɗa, da bayanin wuri).

3.1.3 Bayani mai tushe daga ɓangare na uku

Idan doka ta halatta, za mu tattara bayani game da kai mai tushe daga ɓangare na uku. Misali:

  • Ga wasu ayyukan da ka iya haɗawa da asusun da ma'amaloli na kuɗi, tare da izininka, za mu iya tantance sahihancin bayanin da ka bayar (kamar lambar waya) ta hanyar amfani da ɓangarori na uku don dalilai na tsaro da kariya daga zamba;

  • Ana aikata Haɓaka model na talla ta hanyar keɓantattun bayanan ganewa (kamar IMEI/OAID/GAID waɗanda aka samo daga masu talla) kuma, a wasu halaye, za a yi amfani da bayanan aikin juyarwar da ba a kammala ba (kamar dannawa), wanda ya ke daidai da amfaninka da sabis ɗin talla, don samar da sabis-sabis ɗin talla.

  • Kuma muna iya samo wasu bayanai kamar ID na Asusu, da laƙabi, da hoton bayani, da adireshin imel daga kafafen sada zumunta na ɓangare na uku (misali lokacin da kake amfani da asusun kafar sada zumunta don shiga wani sabis na Xiaomi).

  • Bayani game da kai da wasu suka samar muna, kamar adireshin isar da saƙonka wanda wani mai amfani zai iya samar muna a yayin siyar muku kayayyakinmu ta hanyar sabis-sabis ɗin mi.com.

3.1.4 Bayanin da ba a iya shaida mutum da shi

Kuma muna iya tattara wasu nau'ikan bayanan da ba a danganta kai tsaye ko a kaikaice ga wani mutum ba kuma waɗanda ba za a iya bayyanawa a matsayin bayanin mutum ba bisa ga dokokin gida masu alaƙa. Ana kiran irin wannan bayanin da bayanin da ba a iya shaida mutum da shi. Muna iya tattarawa, da amfani, da turawa, da bayyana ba a iya shaida mutum da shi. Ga wasu misalai na bayanan da muke tattarawa da yadda za mu iya amfani da shi a haɗaɗɗen zubin da a iya shaida mutum da shi:

  • Wannan bayanin na iya haɗawa da bayanan ƙididdigar da aka ƙirƙira a lokacin da kake amfani da wani takamaiman sabis (misali bayanan na’ura waɗanda ba za a iya gane su ba, da amfanin yau da kullun, da ziyarar shafi, da tsawon lokacin shiga shafi, da lamurra masu zango);

  • Bayanan lura da hanyar sadarwa (misali: lokacin nema, adadin nema ko tangarɗar kuskure dss.);

  • Aukuwar gazawar kwatsam ta manhaja (misali: rajistar da aka ƙirƙira bayan gazawar kwatsam ta manhaja).

Dalilin irin wannan tattarawar shi ne don mu inganta sabis ɗin muke samar maka. Nau'i da adadin bayanan da aka tattara ya danganta ne ga yadda kake amfani da kayayyakinmu da/ko sabis ɗinmu.

Muna tattara wannan bayani don samar maka da bayani mai ƙarin amfani da don fahimtar sassan shafin yanar gizonmu, da kayyaki, da sabis-sabis ɗin da ka fi so. Alal misali, muna iya buƙatar sanin adadin masu amfanin da ke amfani a kowace rana, amma ba mu buƙatar sanin wanda ya ke amfani a wannan rana, don haka bayanan da aka tattara sun isa wajen yin nazarin ƙididdiga. Zamu yi ƙoƙarin keɓe bayanin mutum ɗinka daga bayanan da ba a iya shaida mutum da su kuma mu tabbatar cewa ana amfani da nau'ikan bayanan guda biyu a wawware. Duk da haka, idan muka gama bayanan da ba a iya shaida mutum da su tare da bayanan mutum ɗinka, za a ɗauki irin waɗannan bayanan da aka game a matsayin bayanan mutum a ƙarƙashin dokar dokokin sirri da wannan ƙa’idojin sirri muddin dai ya kasance a game.

3.2 Yadda muke amfani da bayanin mutum ɗin da muke tattarawa

Manufar tattara bayanin mutum shine don samar maka da kayayyaki da/ko ayyuka, da kuma don tabbatar da cewa mu bi dokokin, da ƙa’idoji da sauran buƙatun doka. Wannan ya shafi:

  • Samarwa, da sarrafawa, da riƙewa, da ingantawa da kuma bunƙasa kayayyakinmu da/ko sabis a gare ka, kamar isarwa, da kunnawa, da tantancewa, da taimakon bayan cinikayya, da taimakon abokin ciniki da tallatawa.

  • Aiwatarwa da kuma kiyaye matakan tsaro da manufar samar da kariya daga hasara da zamba, kamar gano masu amfani da tantance bayanan shaidar mai amfani. Muna amfani da bayaninka don dalilai na kawar-da-zamba ne kaɗi idan an cika waɗannan sharuɗɗa biyu: akwai buƙatar hakan, kuma bayanan da aka yi amfani da su don kimantawa sun dace da muradun Xiaomi na kare masu amfani da ayyuka.

  • Kula da tambayoyinka ko buƙatunka game da na'urori da ayyuka, kamar amsa tambayoyin abokin ciniki, da aika sanarwar tsarin na’ura da ta manhaja, da gudanar da shigarka a lamurra da tallan rangwame (misali, gasar zaɓen sa'a).

  • Gudanar da ayyukan tallan rangwame masu alaƙa, kamar su samar da kayayyakin kasuwanci da na tallan rangwame da sabuntawa. Idan ba ka son ci ga da karɓar wasu nau’ikan kayayyakin talla, kana iya fita ta hanyar da aka samar a cikin saƙon (kamar su mahaɗin soke rajista na ƙasan saƙo) face idan doka mai alaƙa ta zayyana akasin hakan. Kuma a ɗan duba sashe 9 "mene ne haƙƙoƙin kariyar bayananka" a ƙasa.

  • Dalilai na cikin gida, kamar su nazarin bayanai, da bincike, da kuma ci gaban bayanan ƙididdigar da suka shafi amfani da samfuranmu ko ayyuka don inganta samfuranmu ko sabis. Alal misali, ana aikata koyon inji ko horar da algorizim na model ne bayan an aiwatar da cire bayanan shaida.

  • Inganta aikin na'urarka, kamar nazarin amfani da ma’ajiya ko amfani da CPU na manhajojinka.

  • Ajiyewa da riƙe bayanan masu dangantaka da kai don ayyukan kasuwancinmu (kamar ƙididdigar kasuwanci) ko don sauke nauyin da ke kanmu na doka.

  • Sarrafawa bisa ga halastaccin muradun Xiaomi (a hurumin da dokar ke aiki, alal misali, a ƙarƙashin GDPR). Halastaccin muradu sun haɗa da ba mu damar gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata da kuma samar da kayayyaki da sabis-sabis ɗinmu; da kare tsaron kasuwanci, da tsari, da kayayyaki, sabis-sabis, da abokan cinikinmu (haɗi da dalilai na kariya daga asara da hana zamba); da gudanarwar ciki; da bin ƙa'idoji da matakai na cikin gida; da dai sauran halastaccin muradun da aka bayyana a cikin wannan ƙa’idoji.

    Misali, don tabbatar da tsaron ayyukanmu, da kuma taimaka mana wajen ƙara fahimtar yanayin aikin manhajarmu, za mu iya ɗaukar bayanan da suka dace, kamar yawan amfaninka, da bayanin rajistar gazawa ta kwatsam, da ilahirin amfani, da bayanan aiki, da tushen manhaja. Don hana masu siyarwa marasa izini buɗe na'urori, za mu iya tattara ID na Asusun Xiaomi, da lambar jerangiya da adireshin IP na kwamfutar da ake sarrafawa da kuma lambar jeerangiya da bayanan na'ura na na'urarka ta hannu.

  • Samar da ayyuka na cikin gida a kan na’urorin mai amfani marasa buƙatar sadarwa da sabarmu, kamar amfani da Rubutu a kan na'urarka.

  • Wasu dalilai tare da izininka.

    Ga ƙarin misalai a kan yadda muke amfani da bayananka (wanda ka iya ƙunsar bayanan mutum ɗinka):

  • Aiwatarwa da yi maka rijistar kaya ko sabis-sabis ɗin Xiaomi da aka saya.

  • Ƙirƙira da tanadar asusun Xiaomi ɗinka. Ana amfani da Bayanan sirrin da aka tattara a lokacin da ka ƙirƙiri Asusun Xiaomi a kan shafukan yanar gizonmu ko ta hanyar na'urorin wayar hannunmu don ƙirƙira maka Asusun Xiaomi da shafin furofayil.

  • Sarrafa odar sayayyarka. Ana iya amfani da bayanai game da sayayyar kasuwancin kan itanet don aiwatar da odar sayayya da sabis masu dangantaka na bayan sayayya, haɗi da taimakon abokin ciniki da sake isarwa. Bugu da ƙari, za a yi amfani da lambar oda don duba odar da kyau tare da abokin hulɗarmu mai isar da saƙo, da kuma don ɗaukar bayanan isar da ƙunshin. Za a yi amfani da bayanan mai karɓa, haɗi da suna, da adireshi, da lambar waya da lambar akwatin gidan waya saboda isar da sako. Ana amfani da adireshin imel ɗin don aika maka bayanai na bin sawun ƙunshi. Ana amfani da jerin abubuwan da aka saya don buga imboyis kuma yana ba abokin ciniki damar ganin abun da ke cikin ƙunshin.

  • Kasancewa a cikin Xiaomi Community. Za a iya amfani da bayanan mutum masu alaƙa da Xiaomi Community ko wasu dandamalai na Intanet na Xiaomi don nuna shafin bayanin martaba, da hulɗa tare da sauran masu amfani, da ma’amala a cikin Xiaomi Community.

  • Samar da sabis-sabis na tsarin na’ura. Ana iya amfani da wannan bayanan don kunna sabis-sabis ɗin tsarin na’ura: bayanai masu alaƙa da na'ura ko katin SIM, haɗi da lambar GAID, da lambar IMEI, da lambar IMSI, da lambar waya, da ID ɗin na'ura, da tsarin aiki na na'ura, da adireshin MAC, da nau'in na'ura, da bayanin tsari da gudanar da aiki, da kuma bayanin wuri gami da lambar ƙasa ta wayar hannu, da lambar hanyar sadarwa ta wayar hannu, da lambar yanki ta wuri da kuma lambar gane sel.

  • Binciken matsalolin gazawar kunnawa. Ana amfani da bayanai masu alaƙa da wuri don duba gazawar kunna katin SIM (misali, matsalolin mashiga da hanyar sadarwa ta Sabis ɗin Gajeren Saƙo (SMS)) don gano mai samar da sabis ɗin, da sanar da mai samar da sabis ɗin game da gazawar.

  • Samar da sauran sabis-sabis na tsarin na’ura. Ana amfani da bayanin da aka tattara sa’ad da kake amfani da sabis ɗin tsari na Xiaomi don aiwatar da ayyukan wannan sabis ɗin da samar da inganta sabis, kamar su saukewa, da sabuntawa, da yin rijista, da zartarwa ko inganta ayyukan da suka shafi sabis-sabis ɗin tsarin na’ura. Alal misali, bayanan mutum ɗin da aka tattara ta hanyar Jigogi na iya samar da shawarwarin jigo keɓaɓɓu dangane da tarihinka na saukewa da burauzin.

  • Gano na’urarka. Idan na'urarka ta ɓace ko aka sace ta, fasalin Gano na'ura na Xiaomi zai iya taimaka maka wajen gano ta da tsare ta. Kana iya gano na'urarka a kan taswira ta amfani da bayanin wurinta, ko shafe bayanai daga nesa, ko kulle na'urar. Lokacin amfani da fasalin Gano na'ura, ana ɗaukar bayanan wuri daga na'urar; a wasu yanayi, ana samun wannan bayanin ne daga hasumiya ta sel ko hotspot na Wi-Fi. Kana iya kunna ko kashe wannan fasalin a kowane lokaci a cikin Saituna > Asusun Xiaomi > Xiaomi Cloud > Gano na'ura.

  • Ɗaukar bayanan wuri a cikin hotuna. Kana iya ɗaukar bayanin wurinka a yayin ɗaukar hoto. Za a bayyana wannan bayani a cikin foldar hotunanka kuma za a ajiye wurin da kake a cikin metadata na hotunanka. Idan ba ka son a ɗauki bayanan wurinka a yayin ɗaukar hoto, kana iya kashe wannan a kowane lokaci a saitunan kyamara na na'urar.

  • Samar da fasalolin aika saƙo (misali, Mi Talk, Saƙon Mi). Idan ka sauke kuma ka yi amfani da Mi Talk, za a yi amfani da bayanin da aka tattara ta Mi Talk don kunna wannan sabis ɗin da kuma gane mai amfani da mai karɓar saƙo. Bugu da ƙari, ana adana tarihin tattaunawa don sauƙaƙa sake loda tarihin tattaunawa bayan mai amfani ya sake dasa manhaja, da kuma don daidaitawa a tsakanin na'urori. Ana iya amfani da bayanai kamar lambobin wayar mai aikawa da mai karɓa da ID na Saƙon Mi don kunna sabis ɗin da ba da damar aikin sa na asali, gami da sarrafa saƙonni.

  • Samar da sabis mai alaƙa da wuri. A yayin amfani da sabis ɗin tsarin na’urar Xiaomi, mu ko masu samar da sabis na ɓangare na uku da abokan kasuwanci na iya amfani da bayanin wuri (don ƙarin bayani duba "Yadda muke yaɗawa, da turawa, da kuma bayyana bayanan mutum ɗinka a baina jama'a" a ƙasa) don samar maku da sabis ɗin da kuma samar da cikakkun bayanai game da wannan wurin (kamar cikakkun bayanai na yanayi) a matsayin wani sashe dandamalin Android don kyautata halin aikin mai amfani daidai gwargwado. Kana iya kashe sabis na wuri a cikin Saituna ko kashe amfani da sabis na wuri ga ɗaiɗaikun manhajoji a kowane lokaci.

  • Inganta halin aikin mai amfani ta hanyar nazarin bayanai, da sassan na’ura, da sofwaya. Wasu fasalolin zaɓi, kamar su Shirin Halin aikin Mai Amfani, suna ba Xiaomi damar nazarin bayanai game da yadda masu amfani ke amfani da wayar hannu, da sabis ɗin tsarin na’ura na Xiaomi, da dai sauran sabis-sabis ɗin da Xiaomi ke samarwa, don inganta halin aikin mai amfani, kamar aika rahoton gazawa ta kwatsam. Kuma Xiaomi zai gudanar da nazarin sassan na’ura da sifwaya don inganta halin aikin mai amfani.

  • Samar da fasalin Tsaro. Ana iya amfani da bayanin da aka tattara don fasalolin tsaro da na kula da na’ura a cikin manhajar Tsaro, kamar su Binciken tsaro, da Mai tattalin baturi, da Jerin toshewa, da Mai sharewa, dss. Masu samar da sabis na ɓangare na uku da/ko abokan hulɗar kasuwancinmu ne ke aiwatar da wasu daga cikin waɗannan fasaloli (don ƙarin bayani, duba "Yadda muke yaɗawa, da turawa, da bayyana bayanin mutum ɗinka a baina jama’a" a ƙasa). An yin amfani da bayanin da bayanan mutum ba, kamar jerin bayyanawa na bairos, don ayyukan binciken Tsaro.

  • Samar da sabis na tunkuɗowa. Kuma za a yi amfani da ID ɗin Asusun Xiaomi, da GAID, da lambar FCM, da ID na Android, da kuma ID ɗin Sarari (a kan na'urorin Xiaomi ɗin da aka kunna ma fasalin Sarari na biyu kaɗai) don samar da sabis na tunkuɗowa da sabis na sanarwar Xiaomi don nazarin gudanar aikin tallatawa da aika sanarwowi daga tsari game da sabunta sofwaya ko shelar sabon samfur, haɗi da bayani game da sayarwa da tallace-tallacen rangwame. Don samar maka da sabis ɗin da ke sama, za a tattara bayanan manhaja masu alaƙa (ID ɗin sigar manhaja, da sunan ƙunshin manhaja), kuma za a tattara da bayanan na'ura (samfuri, kamfani) masu alaƙa. Muana iya amfani da bayanan mutum ɗinka saboda aika maka saƙonnin tunkuɗawa (imma ta hanyar aika saƙo a cikin sabis-sabis ɗinmu, ko ta imel, ko ta wasu hanyoyin daban) waɗanda ke nunawa ko tallata kayayyki da sabis-sabis ɗinmu da/ko kayayyaki da sabis-sabis ɗin zaɓaɓɓun ɓangarori na uku. Ana yin wannan ne kawai tare da yardarka, inda ake buƙata a ƙarƙashin dokoki masu dangantaka. Kana iya ficewa daga karɓar bayanan tallace-tallace daga gare mu da ɓangarori na uku a kowane lokaci ta hanyar canza zaɓuɓɓukanka a cikin Saituna, ko gudanar da zaɓuɓɓukanka ta hanyar manhaja/shafin yanar gizo na ɓangare na uku wanda ke amfani da Tunkuɗowar Xiaomi. Kuma ka ɗan duba “Haƙƙoƙinka”a ƙasa.

  • Tantance shaidar mai amfani. Xiaomi na amfani da ECV don tantance shaidar mai amfani da kuma kauce wa shiga asusu ba tare da izini ba.

  • Tattara martanin mai amfani. Martanin da ka zaɓi ka bayar na da muhimmanci wajen taimaka wa Xiaomi yin gyare-gyare ga ayyukanmu. Don bin bahasin matanin da ka zaɓi bayarwa, Xiaomi na iya tuntuɓar ka ta hanyar bayanan mutum ɗin da ka samar kuma ta ajiye bayanan tattaunawar don warware matsala da kyautata sabis.

  • Aika sanarwa. Daga lokaci zuwa lokaci, za mu iya amfani da bayanin mutum ɗinka don aika muhimman bayanai, kamar sanarwa game da sayayya da canje-canje ga sharuɗɗau, da ƙa’idoji, da manufofinmu. Tunda irin waɗannan bayanan suna da mahimmanci ga hulɗarka da Xiaomi, muna ba da shawarar yarda da karɓar waɗannan sanarwowi.

  • Gudanar da ayyukan talla. Idan ka shiga gasar zaɓen sa'a, ko gasa, ko wasu makamantan tallar rangwame ta hanyar dandamalan sada zumunta, za mu iya amfani da bayanin mutum ɗin da ka samar don aika maka kyaututtuka.

  • Samar da keɓaɓɓun sabis-sabis da ƙunshiya, haɗi da tallace-tallace. Don kare sirrinka, muna amfani da bayanan ganewa na musamman maimakon suna, ko imel ɗinka, ko sauran bayanan da ake iya gane ka da su kai tsaye, don samar maka da su keɓaɓɓun kayayyaki, da sabis-sabis, da ayyuka, haɗi da talla.

    Za mu iya haɗa wannan bayanin tare da wasu bayanai daban (ciki har da bayani a tsakanin mabambantan ayyuka ko na'urori irin su, wayoyin hannu, da Na’urorin TV masu basira, da sauran na'urorin da aka haɗa) don samarwa da inganta kayayyaki, da ayyuka, da ƙunshiya, da tallarmu.

    Alal misali, za mu iya amfani da cikakkun bayanai na Asusun Xiaomi a duk ayyukan da kake amfani da su masu buƙatar Asusun Mi. Bugu da ƙari, don haɓaka halin amfaninka da ayyukanmu, tare da bin doka da ƙa'idodi masu dacewa kuma (inda ake buƙata) tare da yardarka, za mu iya tsara bayanai daga mabambantan samfura, ko ayyuka ko kayan aiki daga gare ka ko kuma masu alaƙa da kai don ƙirƙirar laƙabi, wanda za ayi amfani da shi don bayar da shawarwari, da ƙunshiya keɓaɓɓa, da kuma keɓaɓɓun fasaloli.

    Alal misali, za a samar da tallace-tallace keɓaɓɓu dangane da ayyukanka, amfaninka, da zaɓuɓɓukanka masu dangantaka da manhajojinmu da aiyukanmu. Muna ƙirƙirar bayanan martaba ta hanyar nazarin bayanan da aka ambata da kuma ɓangarorin gini (ƙungiyoyi masu takamaiman halaye iri ɗaya) da kuma sanya bayanan mutum ɗinka a sashe ɗaya ko fiye da haka. Ana yin talla keɓaɓɓa ga mutum ne kawai tare da izininka, inda ake buƙatar haka a ƙarƙashin dokoki masu alaƙa. Kana da damar ficewa daga karɓar tallace-tallace keɓaɓɓu da kuma inkarin shirya furofayil, ciki har da wanda aka gudanar don dalilan tallace-tallace na kai tsaye, a kowane lokaci.

    Bisa ga dalilai na gamin da aka ambata da kuma ƙa'idodi na dokoki masu dangantaka, za mu samar maka da wasu mahimman hanyoyin tasarrufi don irin wannan rarrabewa da keɓancewa. Kana da haƙƙin fita-daga karɓar tallace-tallacen kai tsaye daga gare mu da kuma yanke shawara na atomatik. Don aiwatar da waɗannan haƙƙoƙi, kana iya kunna ko kashe waɗannan fasaloli a kowane lokaci a cikin Saituna > Kalmomin sirri & tsaro > Sirri > Sabis ɗin talla ko Saituna > Kalmomin sirri & tsaro > Tsaron tsarin na’ura > Sabis ɗin talla, ko ka tuntuɓe mu ta https://privacy.mi.com/support, ko ka waiwayi hanyoyin sarrafawar da aka bayyana a ƙa’idojin sirri na kowane samfur. Kuma a ɗan duba sashe 9 "mene ne haƙƙoƙin kariyar bayananka" a ƙasa.

4. Ya ya muke yaɗa bayanan mutum ɗinka ga ɓangarori na uku?

Don samar maka da kayayyaki da sabis-sabis ɗinmu, muna iya yaɗa bayanan mutum ɗinka ga amintattun abokan hulɗa ko masu samar da sabis. Alal misali, idan ka yi odar wani samfur a kan sahihin shafin yanar gizonmu, muna yaɗa bayanan mutum ɗinka ga mai samar da sabis na isar da ƙunshi wanda zai gudanar kuma ya aika sayayyarka.

Bugu da ƙari kuma gwargwadon buƙata, Xiaomi zai bayyana bayanan mutum mai alaƙa ga: ma'aikatun gwamnati ko wasu hukumomi masu ikon kafa doka a halin da aka yi takamaimar buƙata gwargwadon doka mai dangantaka; ko hukumomi masu tabbatar da bin doka, a halin da aka yi takamaimar buƙata gwargwadon doka mai alaƙa.

Xiaomi zai bayyana bayanin mutum ɗinka ga waɗannan hukumomi idan doka mai dangantaka ta ba da izini. A dukkan waɗannan halaye, za mu bayyana bayanin da ake buƙata ne kaɗai ga ma'aikatu ko hukumomin da suka cancanta don cim ma halastaccin dalilansu.

Idan akwai buƙata kuma idan doka mai alaƙa ta ba da izini, za mu bayyana bayanan mutum ɗInka ga ma'aikatun da sama son kare kasuwanci, ko haƙƙoƙi, ko kadarori, ko sabis-sabis ɗinmu.

Muna iya yaɗa bayanin mutum ɗinka ga akantoci, ko aditoci, ko lauyoyi, ko sauran ƙwararrin masu ba da shawara na waje waɗanda ke aiki a ƙarƙashin hurumin sirrantawa a hukumance idan muka buƙaci su samar mana da shawarar ƙwararru ko idan doka mai alaƙa ta buƙaci ƙwarewarsu.

Muna iya yaɗa bayanin mutum ga masu zuba jari da sauran kamfanoni masu dacewa a halin siyarwa da gaske ko yiyuwar siyarwa ko wani ciniki mai alaƙa da wani abu a cikin Xiaomi Group.

Don ƙarin bayani game da wannan, tun da kowane samfur ko sabis yana da na shi siffofin, ɗan ziyarci takamaiman ƙa’idojin sirri na kayyaki da/ko sabis ɗin da kake amfani da su.

5. Mene ne madogarar shari'a ta sarrafa bayanan mutum ɗinka?

Muna buƙatar halastacciya madogara ta sarrafa bayanin mutum ɗinka daidai gwargwadon doka. Inda ya dace bisa ga dokar wurin da kake, madogarar doka ta sarrafa bayanan mutum ɗinka a ƙarƙashin Ƙa’idojin Sirri ita ce:

  • Don sauke wajibcin kwangila. Lokacin da ka ƙirƙiri bayanin martaba, ko ka yi rajista ko ka samu dama ga kayyaki Xiaomi ko sabis ɗinsa masi alaƙa, sabis ɗin ne yake ƙayyade dalilan sarrafa bayanin mutum ɗinka kuma za mu sarrafa bayanin mutum ɗinka don mu samu damar samar maka da sabis ɗin. Ɗan lura cewa samar da wasu bayanan mutum ɗinka tilas ne (misali lokacin da aka yi alamar hakan, ko alamar tauraro). Idan ba ka samar da irin wannan bayanan mutum ɗin ba, to ba za mu iya ba samar maka da kayayyaki da sabis-sabis ɗinmu ba.

  • A sakamakon izininka. Kuma kana iya samar mana da bayanin mutum a kan tushen ganin dama don dalilai na samar maka da wannan samfur da sabis ɗinsa masu alaƙa.

  • A kan tushe wajabcin doka na Xiaomi. A matsayin mai sarrafa bayanai, akwai wajibban doka da suka rataya a kan Xiaomi. A wasu halaye (misali don adana bayanin mutum ɗinka a sakamakon husuma ko buƙatar/neman wata hukuma mai sa ido kan kariyar bayanai), sarrafa bayanin mutum ɗinka zai zama dole gare mu don mu samu damar sauke waɗannan wajibai.

  • A gwargwadon iyakar wani halastaccen muradi. A wani lokaci, la'akari da mafi ƙarancin tasirin sirri a gare ka, akwai buƙatar sarrafa bayanin mutum ɗinka don halastaccin muradu masu zuwa:

    • Tsaron tsarin bayanai, tsaro na hanyar sadarwa, da tsaro na yanar gizo a cikin Xiaomi.

    • Don inganta tsaron tsarin na’ura, da hana zambar tarko ta yanar gizon, da kuma kare tsaron asusun.

    • Ayyukan kamfani, da yin binciken ciki-da-bai, da binciken cikin gida (musamman, masu alaƙa da tsaron bayanai da/ko sirri).

    • Haɓakawa da inganta samfur (gami da bincike da inganta sattuna ko fasalolin Asusun Xiaomi).

6. Waɗanne matakan tsaro muke bi don kare bayanan mutum ɗinka?

6.1 Matakan kariyar tsaro na Xiaomi

Mun ɗauki alƙawarin tabbatar da amincin bayanan mutum ɗinka. Don hana samun dama mara izini, ko bayyanawa ko makamantan haɗura, mun tanadi dukkan matakai na zahiri, da na lantarki, da kuma na gudanarwa, waɗanda doka ta buƙata don karewa da tsare bayanan da muka tattara daga gare ka. Za mu tabbatar da cewa mun kiyaye bayananka na sirri gwargwadon doka mai dangantaka.

Misali, lokacin da kake shiga Asusun Xiaomi dinka, za ka yi amfani da tsarin tantancewa mai matakai biyu don ƙara ƙarfafa tsaro idan asusunka yana cikin kasada. Idan ka aika ko ka karɓi bayanai daga na'urar Xiaomi zuwa sabarmu, muna tabbatar da cewa an baddalar da su ta hanyar amfani da Transport Layer Security ("TLS") da sauran fasahohin algorizim.

Ana adana dukan bayanan mutum ɗinka a kan saba mai tsaro, kuma ana kare su a wurare masu samun kula. Muna karkasa bayananka bisa ga muhimmanci da ƙarfin sirrinsu, kuma muna tabbatar da bayanin mutum ɗinka ya samu matakin tsaron da ya ke buƙata. Muna da hanyoyin tace damar shiga na musamman ga ma'ajiyar bayanai ta gajimare, kuma muna yin bitar yadda muke tattarawa, da ajiyewa, da sarrafa bayanai a-kai-a-kai, haɗi da matakan tsaro na zahiri, don kawar da duk wani yunƙurin shiga ko amfani mara izini.

Duk da haka, ya kamata ka sani cewa amfani da Intanet ba shi da cikakken tsaro, kuma saboda wannan dalili ba za mu iya tabbatar da tsaro ko aminci na kowane bayananka na sirri da ka aika ko aka aika maka ta Intanet ba.

Muna gudanar da ƙwarewa ga abokan hulɗa da masu bada sabis na ɓangare na uku don tabbatar da cewa suna iya kare bayananka na sirri Har ila yau, muna duba cewa wajibi ne wadannan kamfanonin ke kiyaye takardun tsaro masu dacewa ta hanyar sanya takunkumin kwangila masu dacewa, kuma idan ya cancanta, gudanar da bincike. Bugu da ƙari, ma'aikatanmu da abokan kasuwancinmu da masu bada sabis na ɓangare na uku waɗanda ke samun damar bayananka suna ƙarƙashin biyan bukatun kwangila. Muna gudanar da horarwa da tsare sirrin tsaro da kuma gwaje-gwajen don inganta aikin ma'aikatanmu game da muhimmancin kare bayananka na sirri. Za mu dauki matakai da doka da suka dace don kiyaye bayananka na sirri.

Idan kutsen bayanan mutum ya auku, muna cika buƙatar doka kamar yadda ya ke a dokar kare bayanai mai alaƙa wadda ta ƙunshi, sanar da kutsen ga hukuma mai sa ido ga kariyar bayanai da masu bayanan, a halin da akwai buƙatar haka.

6.2 Abin da za ku iya yi

Kana iya saita kalmar sirri ta musamman ga sabis ɗin Xiaomi ta hanyar ƙin bayyana kalmar sirrin shiga ko bayanin asusunka ga kowa (sai dai idan ka bai wa mutumin izini) don guje wa fallasar kalmar sirri ga shafukan yanar gizo waɗanda ke iya yin illa ga tsaron asusunka a Xiaomi. A duk lokacin da zai yiwu, don Allah ka da ka bayyana lambar tabbatarwar da ka karɓa ga kowa (haɗi da waɗanda suka yi iƙirarin su ma’aikatan sabis na abokin ciniki na Xiaomine ). Duk lokacin da ka shiga a matsayin mai amfani da Asusun Xiaomi a kan wannan Dandamali, musamman a kan kwamfutar wani ko kuma a kan tashoshin intanet na jama'a, ya kamata koyaushe ka fitar da asusu a ƙarshen zangonka. Ba za a iya kama Xiaomi da alhakin giɓin tsaro da faru sanadiyyar wasu bangarori na uku sun shiga bayanan mutum ɗinka sakamakon kasawarka ta kiyaye sirrin bayanan mutum ɗinka. Duk da haka, ya kamata ka sanar da mu nan da nan idan akwai wani shige ko amfani mara izini ga asusunka daga kowane mai amfani da Intanet ko wani kutse ga tsaro. Taimakonka zai fabe mu a wajen kare bayananka na sirri.

6.3 Dama ga wasu fasaoli a kan na'urarka

Manhajojinmu na iya samun dama ga wasu fasaloli na kan wayarka. Ana amfani da wannan bayanin don bada dama ma manhaja ya gudana a kan na'urarka kuma ya ba ka damar hulɗa tare da manhaja. Kana iya soke izininka a kowane lokaci ta hanyar kashe su a matakin na'urar ko ta hanyar tuntuɓar mu ta https://privacy.mi.com/support.

7. Mene ne tsawon lokacin da ake adana bayanan mutum ɗinka?

A matsayin ƙa’idar gama-gari, muna riƙe bayanin mutum na tsawon lokacin da ake buƙata ga dalilan da aka bayyana a cikin wannan ƙa’idojin sirri, ko kamar yadda doka ta buƙata. Za mu daina riƙewa bayanin mutum ɗinka kuma mu goge su ko mu cire musu bayanan shaida da zarar an kammala dalilin tattarwa, ko bayan mun tabbatar da neman sharewa daga gare ka, ko bayan mun tsayar da aikin sabis-sabis masu alaƙa, face idan akwai buƙata ko izinin doka mai alaƙa, a wannan hali za mu keɓe bayanin mutum ɗinka kuma ba za a ƙara sarrafa shi ba sai idan akwai bijirowar buƙatar doka da sauran dalilai waɗan da doka mai alaƙa ta ba izini. A irin wannan yanayi, ana iya samar da bayanin mutum ɗinka ga ɓangarorin da doka mai alaƙa ta ba izini. Da zarar daidaitattun lokutan riƙewa sun wuce, irin waɗannan bayananka na sirri za a goge ko ɓoye sunansu.

8. Ta ya za ka iya gudanar da zaɓuɓɓukan sirrinka?

Mun gane cewa damuwa akan bayannan sirri na da bambamci dagane da mutum zuwa mutum. Sabo da haka, muna samar da misalan hanyoyin da za ka iyakance tattarwa, ko amfani, ko bayyanawa, ko sauran ayyukan sarrafa bayanin mutum ɗinka da kuma sarrafa saitunan sirrinka:

  • Duba kuma ka sabunta bayanan tsaro na asusunka, da bayanin mutum ɗinka, da izini, da gudanar da na'ura a kan na'urarka a cikin Saituna > Asusun Xiaomi, ko ta hanyar shiga https://account.xiaomi.com;

  • Duba kuma ka sabunta bayaninka a cikin asusun wannan Dandamali a Asusuna > Gyara bayani;

  • Sabunta zaɓuɓɓukan sanarwa a cikin asusun wannan Dandamali a Asusuna > Zaɓuɓɓukan Sanarwa;

  • Soke sabis ko asusu. Idan ka so soke Asusun Xiaomi ɗinka, kana iya yin hakan ta bin matakan da ke cikin Saituna > Asusun Xiaomi >Taimako > Share Asusu, ko ta ziyartar https://account.xiaomi.com;

  • Idan a baya ka ba yarda da mu yi amfani da bayanin mutum ɗinka don dalilan da aka zayyana ƙa’idojin sirri masu alaƙa, kana iya sauya ra'ayinka a kowane lokaci ta hanyar tuntuɓar mu a kan https://privacy.mi.com/support.

Lura cewa soke Asusun Xiaomi ko furofayul ɗinka zai hana ka yin amfani da cikakken jerin gwanon samfuran Xiaomi da sabis-sabis masu alaƙa da shi. Don kare halastaccin haƙƙoƙi da muradunka ko na wani, za mu yi nazarin yiwuwar samar da nemanka na sokewa bisa ga amfaninka da mabambantan kayayyaki da sabis-sabis na Xiaomi.

9. Mene ne haƙƙoƙin kariyar bayananka?

Kana da wasu haƙƙoƙi dangane da bayanin mutum ɗinka na game da kai wanda muke riƙe da shi (wanda ake kira "nema" a nan). Da fatan za a lura cewa ya danganta da inda kuka kafa, waɗannan haƙƙoƙin za su kasance ƙarƙashin keɓance takamaiman keɓancewa da a ƙarƙashin ƙa'idodin gida:

  • Haƙƙin dama ga/samun rahoto mai fayyace bayanin mutum ɗinka na game da kai wanda muka riƙe da shi. Za a samar maka da kwafin bayanin mutum ɗinka da muka sarrafa idan ka nema ba tare da biyan kuɗi ba. Don wani ƙarin buƙatar bayani mai alaƙa, muna iya sanya farashi mai ma’ana bisa ga ainihin farashin gudanarwa gwargwadon doka mai alaƙa. A kowane hali dai, ɗan lura cewa kana iya shiga Ausun Xiaomi da/ko wannan Dandamali don binci wasu bayanan mutum ɗinka waɗanda muka riƙe maka.

  • Haƙƙin gyara bayanin mutum ɗinka. Idan duk wani sakon da muke rikewa ba daidai bane ko kuma bai cika ba, kana da damar da zaka iya samun bayananka na sirri daidai ko kuma cikakke ta wannan hanyar tare kamar haka. Lura cewa kana iya kuma iya shiga Asusun Xiaomi da/ko wannan Dandamali don gyara wasu bayananka.

  • Haƙƙin share bayanin mutum ɗinka. Bisa ga buƙatun dokokin da suka dace, kana da haƙƙin neman gogewa ko cire bayanin mutum ɗinka a inda babu wani ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sa mu ci gaba da amfani da shi. Za mu yi la'akari da dalilai game da buƙatar ku na sharewa kuma mu ɗauki matakai masu ma'ana, gami da matakan fasaha, don ci gaba da goge bayananka na sirri. Ɗan lura cewa ƙila ba za mu iya cire bayanan nan take daga tsarin ajiyar madadi ba saboda doka mai dacewa (misali, idan ya akwai buƙatar adana bayanin mutum ɗinka don yuwuwar ƙarar da za ka iya tasowa daga ko dangane da sarrafa irin waɗannan bayanan mutum ɗinka) da/ko iyakokin fasaha. Idan haka al’amarin ya ke, za mu adana bayanin mutum ɗinka cikin aminci kuma mu keɓe shi daga duk wani ƙarin sarrafawa har sai an an samu damar goge bayanin ko cire masa bayanan shaida.

  • Haƙƙin inkarin sarrafa bayanin mutum ɗinka. Kana da haƙƙin yin inkari, a kan dalilai masu alaƙa da halinka, ga sarrafa bayanin mutum ɗinka wanda ya ke da dangantaka da halastaccen muradin Xiaomi, ko wasu dalilai na doka waɗanda doka mai alaƙa ta ba da izini. Idan ka yi inkarin irin wannan sarrafawa, ba za mu ci gaba da sarrafa bayananka ba bisa waɗannan daliai sai in doka mai dangantaka ta ba mu izini.

  • Haƙƙin iyakance sarrafa bayanin mutum ɗinka. Kana da haƙƙin iyakance mana sarrafa bayanin mutum ɗinka, alal misali, idan sarrafawar ba halastacciya ba ce a fahimtarka, amma kuma kana inkarin shafe bayanin mutum ɗinka. A irin waɗannan halaye, za a sarrafa bayanin mutum ɗinka tare da amincewarka, don neman haƙƙi ko inkarin masu iƙirarin haƙƙi ko don/a ƙarƙashin wasu dalilai na doka waɗanda doka mai dangantaka ta ba da izini.

  • Haƙƙin samar da bayanai a siffa mai ɗaukuwa. A wasu yanayoyi da doka ta samar, kana da haƙƙin karɓar bayanin mutum ɗin da ya shafe ka a siga mai kamala, wadda ake yawan amfani da ita kuma wadda injin zai iya karantawa da/ko a watsa wannan bayanin mutum zuwa wani mai sarrafa bayanai.

  • Haƙƙin janye izini. A halayen da ake buƙatar izininka don sarrafa bayanin mutum ɗinka, kana iya janye amincewarka a kowane lokaci. Sai dai kuma, ɗan lura cewa idan ka janye izininka, to wataƙila ba za ka iya ci gaba da amfani da Dandamalin da sabis mai alaƙa da shi ba, da/ko samun dama ga wasu bayanai, ko fasaloli. Janye izinin ka ko bada izini ba zai shafi ingancin tarin mu ba da sarrafawa da aka yi bisa yarda har zuwa lokacin janyewa.

  • Sauran haƙƙiƙi a ƙarƙashi doka mai dangantaka.

Ɗan tuna cewa kana kuma shiga, da sabuntawa, da share wasu bayanan da suka danganci bayanin mutum ɗinka a cikin Asusun Xiaomi a https://account.xiaomi.com ko ta shigar da Asusun Xiaomi ɗinka a kan na’urarka. Don ƙarin bayani, ɗan aiko mana rubuta ko ka tuntuɓe mu ta hanyar https://privacy.mi.com/support.

10. Ya za ka bi haƙƙin kariyar bayananka kuma ya za ka tuntuɓe mu?

Idan kana da wani tsokaci ko tambayoyi game da wannan Ƙa’idojin Sirri ko wasu tambayoyi da suka shafi tattarawar Xiaomi, da amfani ko bayyana bayanin mutum ɗinka, ko kana son bin haƙƙoƙin kariyar bayananka bisa ga Sashen da ke sama, saki jiki ka tuntuɓe mu ta hanyar ziyartar https://privacy.mi.com/support ko a adiresoshin da ke ƙasa (a aika buƙatarka a rubuce). Idan muka karɓi tambayoyi game da bayanin mutum ko buƙatun saukewa ko dama ga abubuwa, muna da tawagar ƙwararru da ke magance irin waɗannan matsalolin, gami da Jami'an Kariyar Bayanai (DPOs), waɗanda ake iya tuntuɓar ta https://privacy.mi.com/support ko a adiresoshin gidan waya na ƙasa. Idan tambayarka ta ƙunshi wani matsala mai muhimmanci, za mu iya tambayarka don ƙarin bayani. Idan ka tuntube mu, za mu samar da bayanai game da tashoshi da aka dace da za su iya dacewa bisa ga halin da kake ciki.

  • Ga masu amfani mazauna Yankin Tattalin Arziki na Turai (EEA), da UK, da kuma CH:

Xiaomi Technology Netherlands B.V., Prinses Margrietplantsoen 39, 2595 AM, Hague, Ƙasar Netherlands

  • Ga masu amfani mazauna Indiya:

Xiaomi Technology India Private Limited, Building Orchid, Block E, Embassy Tech Village, Outer Ring Road, Devarabisanahalli, Bengaluru, Karnataka - 560103, Indiya

Duk wani rashin daidaito da korafi dangane da aiki da bayanan sirri ko bayanai za a sanar da shi ga Jami'in Korafi na Musamman kamar yadda aka ambata a kasa:

Suna: Vishwanath C

Tarho: 080 6885 6286, Lit-Asa 9 Safe to 6 Yamma

Imel: grievance.officer@xiaomi.com

  • Ga masu amfani mazauna sauran ƙasashe/yankuna:

Xiaomi Technologies Singapore Pte. Ltd. 1 Fusionopolis Link #04-02/03 Nexus@one-north, Singafo 138542

Ɗan tabbatar da cewa ka samar da isassun bayanai don ba wa Xiaomi damar tantance shaidarka da kuma tabbatar da cewa kai mamallakin bayanan, ko kana da izinin doka na wakiltar mamallakin bayanan. Da zarar mun samu isasshen bayanin da ya tabbatar muna za a iya sarrafa buƙatarka ta saukewa, za mu zarce don amsa buƙatarka a cikin tsawon lokacin da aka shata a ƙarƙashin dokar kariyar bayanai mai dangantaka gare ka.

Muna da 'yancin dakatar da aiwatar da buƙatun da ba su da mahimmanci, a fili mara tushe ko wuce gona da iri, buƙatun da za su lalata haƙƙin sirri na mutane, ƙididdigar da ba daidai ba, da buƙatun da suke buƙatar aikin fasaha maras dacewa, da kuma buƙatar ba a buƙata a ƙarƙashin dokokin gida, bayanan da aka gabatar da jama'a, da kuma game da bayanan da aka bayar ƙarƙashin sharuɗɗan sirri. Idan muka yi imani cewa wasu bangarori na buƙatar don sharewa ko samun dama ga bayanai zai iya haifar da rashin iyawarmu don yin amfani da bayanan da aka yi amfani da shi game da cin zarafi da dalilai na tsaro, ana iya ƙin yarda. Za mu sanar da ku duk irin wannan yanke shawara na kin aiwatar da buƙatarku da kuma dalilin wannan shawarar idan doka ta buƙata, a yayin da za mu sanar da ku a cikin kowane lokaci da aka tsara a ƙarƙashin doka mai dacewa.

Idan ba ka gamsu da amsar da ka karɓa ba, kana iya miƙa damuwar zuwa hukuma mai kafa doka ta yankinka. Idan kana zaune a EEA/UK/CH ne, ɗan duba jerin manyan hukumomi EEA/UK/CH masu alhaki a nan.

11. Ya ya ake tura bayanan mutum ɗinka daga a da ƙasa zuwa ƙasa?

Hanyar Xiaomi da kuma ci gaba da bayanan sirri ta hanyar aikin sarrafawa a duniya. Yanzu, Xiaomi yana da su cibiyoyin bayanai a Indiya, Holand, Jamus, Rasha da Singapore. Don dalilai da aka bayyana a cikin Sharuddan Bayanai, za a iya sauke bayaninka zuwa waɗannan cibiyoyin bayanai bisa ga doka mai dacewa.

Ƙila mu iya canja bayaninka na sirri ga masu bada sabis na ɓangare na uku da abokan kasuwanci kuma ana iya ƙaddamar da bayaninka ga wasu ƙasashe ko yankuna. Yankunan doka, waɗannan kamfanonin duniya da masu samar da sabis na ɓangare na uku ke zaune, ka iya ko su ƙi kare bayanin mutum a mataki iri ɗaya da yadda yankin dokarka zai yi ba. Akwai mabambantan kasadodin haɗari a ƙarƙashin mabambantan dokokin kariyar bayanai kuma za mu iya turawa ko adana bayanin mutum ɗinka zuwa kamfanonin ƙasar waje, duk da cewa, wannan ba zai sauya alƙawarinmu na bin wannan Ƙa’idojin Sirrin ba da kuma kare bayanin mutum ɗinka.

Musamman ma:

  • Ana sarrafa da adana bayanin mutum ɗin da muke tattarawa da ƙirƙira a ayyukanmu a Rasha a cibiyoyin bayanai masu mazauni a Rasha, face na watsawa a wajen boda wanda dokar Rasha ta ba da izini.

  • Ana adana bayanin mutum ɗin da muke tattarawa da ƙirkira a cibiyoyin bayanai masu mazauni a Indiya.

Idan muna buƙatar tura bayanin mutum wajen hurumin dokarka, imma zuwa abokan haɗin gwiwarmu ko masu samar da sabis na ɓangare na uku, ko abokan kasuwanci, za mu bi dokoki masu alaƙa. Muna tabbatar da cewa duk irin wannan canja wurin yana biyan bukatun dokoki masu kariya na bayanan gida ta hanyar aiwatar da kariya ta gari. Kana iya ganin matakar kariyar da muke da su ta hanyar tuntuɓar mu a https://privacy.mi.com/support.

Idan kana amfani da ayyukanmu a cikin EEA, UK ko CH. Xiaomi Technology Netherlands B.V. zai yi aiki a matsayin mai sarrafa bayanai shi kuma Xiaomi Technologies Singapore Pte. Ltd. zai kasance mai alhakin sarrafa wasu daga cikin bayanan mutum ɗinka. Idan Xiaomi ya yaɗa bayanin mutum ɗinka wanda ya samo asali daga gare ka a cikin EEA, UK, ko CH zuwa wani sashen Xiaomi Group, ko masu samar da sabis na ɓangare na uku, ko abokin kasuwanci a wajen EEA, UK, ko CH (ɗan duba Sashe na 4 na sama don ƙarin bayani), inda wataƙila dokar yankin ba ta samar da kariya ga bayanin mutum ɗinka a mataki iri ɗaya da na ƙasarka ko yankinka, Xiaomi zai yi amfani da Daidaitacciyar Dokar Yarjejeniya ta EU ko kowane irin matakin kariyar da aka samar a GDPR ko a dokokin UK ko CH masu dangantaka don kare bayaninka ta bin mafi ingacin matakan Turai.

12. Ya ya ake kare ƙananan yara?

Muna la'akari da alhakin iyaye ko mai kulawa don kula da amfani da yaro da samfurori ko ayyukanmu. Ba ma samar da sabis-sabis kai tsaye ga yara ko amfani da bayanin mutum na yara don dalilai na talla.

Idan kai mahaifi ne ko mai riƙo kuma kana jin wani yaro ya bayar da bayanin mutum ɗinsa ga Xiaomi, ɗan tuntuɓe mu ta https://privacy.mi.com/support don tabbatar da cewa an cire bayanin mutum ɗin nan take da kuma cewa an soke rijistar yaron daga duk wani sabis ɗin Xiaomi mai alaƙa.

13. Shin dole ne sai ka yarda da wani sharaɗi da ƙa’idar ɓangarori na uku?

Sharuddan Bayanan mu ba ya shafan kaya da sabisin da wasu ke badawa. Dangane da sabis ɗin kake amfani da shi, wasu na iya ƙunsar kayayyaki ko sabis-sabis na ɓangarori na uku kamar su sabis-sabis ɗin sarrafa biya kuɗi, dss. Za a samar da wasu daga cikinsu a siffar mahaɗai zuwa shafukan yanar gizo na ɓangarori na uku, kuma za a samu damar shigar su ne a siffar SDKs, APIS, dss. Kuma waɗannan ɓangarorin na uku ka iya tattara bayananka idan ka yi amfani da waɗannan kayayyaki ko sabis-sabis. Saboda wannan dalili, muna bada shawara mai karfi cewa ka dauki lokaci ka karanta sharuddan bayanai na wancan bangaren kamar yadda ka dauki lokaci ka karanta namu. Ba mu daukar nauyi kuma baza mu iya sarrafa yadda wasu bangare daban ke amfani da bayananka sirri da suka tattara daga gare ku ba. Sharuddan Bayanan mu ba ya shafan wasu shafukan da aka hada daga sabisin mu.

14. Ya ya muke sabunta Gama-garin Ƙa’dojin Sirri?

Mukan yi bitar Ƙa’idojin Sirri lokaci-lokaci bisa ga sauye-sauyen kasuwanci, da na fasaha, da na doka mai dangantaka da kuma yanayin kyautatuwar aiki, kuma muna iya sabunta wannan Ƙa’idojin Sirri. Idan muka yi mahimmin sauyi ga ga wannan Ƙa’idojin Sirri, za mu sanar da kai hanyar taga mai ɓullowa, ko ta aika imel zuwa adireshin imel mai alaƙa ga Asusun Xiaomi ɗinka ko ta wata halastacciyar hanya kuma mai samuwa, don ku samu damar fahimtar bayanin da muka tattara da yadda muke amfani da shi. Irin waɗannan sauye-sauye ga wannan ƙa’idojin Sirri za su fara aiki daga kwanan watan kama aiki wanda aka zayyana a saman sanarwar. Muna ƙarfafa ka don duba wannan shafin lokaci-lokaci don sabon bayanin game da ayyuka na bayanan sirrinmu. A wurin da doka mai dangantaka ta buƙata, za mu tambaye ka bayanannen izininka idan za mu tattara ƙarin bayanin mutum daga gare ka ko idan za mu yi amfani ko bayyana bayanin mutum ɗinka don sabbin dalilai.